Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun sauraron korafin za?en shugaban ?asa ta ?age zamanta zuwa 30 ga watan Mayu kan kalubalantar sakamakon za?en watan Fabrairu.
Hakan na nufin sai an rantsar da sabon shugaban ?asar, Bola Tinubu, a ranar Litinin, 29 ga wata kafin ci gaba da sauraron shari’ar.
Hakan ya biyo bayan kin amincewa da bukatar ya?a hukuncin kotun ta talabijin da masu orafin suka shigar.
Hukumar za?en ?asar ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe za?en shugaban ?asar da aka gudanar.
Kafin ta ?age zaman nata a yau Talata, kotun ta ha?e ?orafe-?orafen da jam’iyyun adawa na PDP da Labour da APM ke yi game da nasarar Tinubu.
A ranar Litinin mai zuwa ne za a rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.
Kotun sauraron ararrakin za?en da ta fara zama mako biyu da suka gabata, ta ce tana da wata uku don sauraron shaidu da kuma yanke hukunci kan ?orafe-?orafen.
‘Yan takarar adawa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour Party, na son a yi watsi da sakamakon za?en shugaban ?asar, inda suke zargin cewa an tafka magu?i.
