An Kakaba Sabon Harajin Kiran Waya Ga ‘Yan Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta kallafa sabon harajin kiran waya a kasar nan domin daukar nauyin kiwon lafiyar masu rauni a Najeriya.

An ruwaito cewa, wannan ya biyo baya yunkurin da kamfanonin sadarwa suka digan yi a cikin kwanakin nan na kara kudin kira sakamakon halin da suka tsinci kansu a kasar nan.

Harajin wayar na daidai da kwabo daya a duk dakika daya kuma yana daga cikin hanyoyin samun kudin da za a dauki nauyin kiwon lafiya na kyauta ga masu rauni a Najeriya.

Wannan na kunshe a sabuwar dokar Inshorar Kiwon lafiya ta 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a makon da ya gabata.

Dokar ta hada da tanadin sashi na 26, karamin sashi na 1c wanda ya ce inda za a samo kudin domin kungiyoyi masu raunin ya hada da harajin sadarwa wanda bai gaza kwabo daya ba a kowacce dakika na kiran waya.

Related posts

Leave a Comment