Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya saka tukwicin naira miliyan 10 ga duk mutum ko kungiyar da za ta bayar da bayanai masu amfani da zai kai ga kama makasan dan majalisar dokokin jihar, Hon Okechukwu Okoye.
Idan za a tuna an yi garkuwa da mamba mai wakiltan mazabar Gwamna Chukwuma Soludo, Hon Okechukwu Okoye, a makon da ya gabata.
Sai dai kuma, an tsinci kansa a ranar Asabar, 21 ga watan Mayu, a Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra, ba tare da gangar jikinsa ba.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren labaran gwamnan, Mista Christian Aburime kuma aka gabatar da ita ga manema labarai a daren Asabar, gwamnan ya saka tukwicin naira miliyan 10 kan makasan dan majalisar.
A cewar gwamnan, an yi garkuwa da Hon Okoye da Cyril Chiegboka a kan hanya a ranar 15 ga watan Mayu. Ya jajantawa ‘yan uwansa Isuofia, yana mai cewa mai yiwuwa wadannan miyagun da suka kai masa hari tare da kashe ‘yan sanda uku a Isuofia shekaru biyu da suka wuce ne suka kara kaddamar da wannan harin.
Soludo ya sha alwashin cewa dole ne a kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika da duk masu aikata laifuka a Anambra tare da hukunta su.
