Takarar Sanata: Ina Nan Daram Ban Janye Ba – Rabi Salisu Ibrahim

‘Yar takarar kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC Hajiya Rabi Salisu Ibrahim ta bayyana cewar tana nan akan aniyar ta ta neman Kujerar Sanatan ba ta janye wa kowa ba.

Rabi Salisu Ibrahim ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wani taron manema labarai da ta kira a Kaduna biyo bayan jita jitar da wasu ke ya?awa na cewar wai ta janye daga takarar.

‘Yar Siyasar ta kara da cewar ita ce ta farko a yankin da ta sayi Fom na tsayawa takara, kuma a matsayin ta na ‘yar gwagwarmaya ba zata janye wa kowa ba har sai an kammala zaben fidda gwani.

“Kwanan nan ?ungiyar Kansilolin shiyar Kaduna ta tsakiya suka za?e ni a matsayin ‘yar takarar da suka amince da ita ta nemi wannan Kujera saboda gamsuwa da cancanta ta bisa ga haka ina nan daram a takarar Sanata”.

Dangane da batun cewa Gwamnan jihar Kaduna El Rufa’i ya nuna sha’awar sa ga wani ?an takara domin neman kujerar Sanatan, Rabi Salisu Ibrahim ta ce Gwamnan ya bukaci ?an takarar ya je ya nema ne amma ba wai ya sahale mishi Kujerar bane, saboda haka nema babu fashi ?angaren ta.

“Matsayina ta ‘yar gwagwarmaya wadda ta san harkar tsaro mai taimakon Mata da Marayu ni nafi dacewa da wannan Kujera, domin kawo cigaba a mazabata wadda take fama da ?alubalen tsaro”.

Related posts

Leave a Comment