Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da babban zabe na 2023 ke kara matsowa, Kungiyar Harkokin Matasan Najeriya (YNNU) ta rubuta wasika ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan tana bukatar ya koma jam’iyyar APC.
Shugaban kungiyar na kasa, Ibrahim Saiki, a ranar Laraba, 27 ga watan Afirilu ya shaida yadda kungiyar ta aika wa Jonathan da wasika tana bukatar ya yi rijistar jam’iyyar APC a gundumar Otuoke da ke Bayelsa sannan ya siya fom din tsayawa takarar shugaban kasa na 2023.
Saiki ya shaida yadda kungiyar ta bai wa tsohon shugaban kasar wa’adin mako daya bayan watan Ramadan, a cewarsa, in har Jonathan ya gaza yin hakan, mambobin kungiyar za su je har ofishinsa da ke Abuja su mamaye shi har sai ya yanke shawarar.
“Muna mika rokonmu da bukatarmu ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan akan yin gaggawar komawa jam’iyyar APC a gundumarsa ta Otuoke da ke Bayelsa cikin kwana 7 bayan watan Ramadan.
“In har kwanakin suka kare kuma Jonathan bai dauki wani mataki ba, za mu yi abinda ya dace ta hanyar zuwa ofishinsa don yin tursasashi. “Abin kula anan shi ne yadda fiye da mutane 20,000 cikin manyan mambobin kungiyarmu 500,000 da ke kasar nan suke a shirye da su shiga dumu-dumu kuma su mamaye ofishin Jonathan.
Sannan zamu ci gaba da zama har sai ya bayyana mana matakin da ya dauka.”
