Daren Lailatul Kadri: Aisha Buhari Ta Yi Wa Najeriya Addu’ar Samun Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwargidan shugaban ?asa Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa ?asa Najeriya addu’ar samun dorewar tsaro a kwanakin ?arshe na watan azumin Ramadan.

Hakazalika Uwargidan Shugaban ?asar ta ambaci al’ummar jihar Zamfara dake fama da matsalar tsaro da sauran jihohin da fitinar ‘yan Bindiga ke addaba faddu’ar samun dawwamammen zaman lafiya.

Aisha Buhari ta wallafa sakon ne a daren Laraba, inda ta roki Allah ya samar wa mutanen jihar har da sauran ‘yan kasar mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a lokacin da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Kadri.

“Allah ya fitar da mu da mutanen jihar Zamfara daga cikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Kadri, Ameen!”

Related posts

Leave a Comment