Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci jam’iyyar PDP da ta bashi dama a zaben fidda dan takararta na shugaban kasa saboda shine dan takara mafi cancanta da zai kawo mata kujerar.
Da yake jawabi ga ‘ya’yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, Atiku ya ce ya kamata a yi la’akari da shi saboda tuni ya mallaki kuri’u miliyan 11 da ke jiransa.
“Ni ne dan takara mafi cancanta. A tashin farko ni dake tsaye a gabanku mutum ne wanda kuri’u miliyan 11 ke jiransa. Kuma ina ganin, a matsayin jam’iyya, ya kamata ku bani dama a tashin farko amma muna a tsari ne na damokradiyya.
“Abun da zan bukace ku shine ku tabbatar da ganin cewa ku ci gaba a yadda ku ka fara, kuma ku kammala ta hanyar zama adalai, masu gaskiya da kuma ba dukkanin yan takara damar fuskantar masu zabe.”
