Adamawa: An Damke Mutumin Da Ya Hallaka’Ya’yansa Ta Hanyar Jifa

Labarin dake shigo mana daga jihar Adamawa na bayyana cewar rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama wani mutum da ake zargi ya jefe ‘ya’yansa biyu da kuma dukan su da sanda har sai da suka mutu.

Ana zargin mutumin mai suna Elisha Tari mai shekara 25 da yi wa ‘ya’yan nasa duka, mai shekara biyu da mai shekara uku, bayan sun rabu da mahaifiyarsu wata biyu da suka wuce.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar ranar Asabar, binciken farko-farko da aka gudanar sun nuna cewa mutumin mazaunin ?aramar Hukumar Michika, ya kashe yaran ne bayan sun samu sa?ani da mahaifiyarsu.

Ana zargin ya yi amfani da sandar kuma ya yi ta dukan su a ka. Hotunan da rundunar ta wallafa sun nuna yaran kwance, kansu duk ?ura da kuma jini.

An kama wanda ake zargin ne yayin da yake yun?urin tsallakawa zuwa ?asar Kamaru mai ma?wabtaka, a cewar ‘yan sanda, kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike don gano ainahin abin da ya faru.

Related posts

Leave a Comment