Wani Bangare Na Ma’aikatan Jami’a Sun Janye Yajin Aiki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyoyin ma’aikata biyu na jami’o’in Gwamnatin Tarayya sun janye yajin aiki bayan ganawar su da Ministan Ilimi Adamu Adamu ranar Asabar.

Kwamatin ha?in gwiwa da ?ungiyoyin Senior Staff Association of Nigerian Universities da Non-Academic Staff Union of Educational and Allied Institutions ne suka gana da ministan a Abuja.

Sai dai azuzuwan jami’o’in gwamnatin za su ci gaba da kasancewa a rufe saboda ?ungiyar malaman jami’a ta ASUU ba ta janye nata yajin ba wanda ta shafe fiye da wata biyar tana yi.

?ungiyoyin biyu sun fara nasu yajin aikin a watan Maris jim kadan bayan ASUU ta fara nata.

Shugaban ?ungiyar SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim, ya fa?a wa manema labarai cewa sun jingine yajin aikin ne tsawon wata biyu da zimmar bai wa gwamnatin tarayya damar aiwatar da al?awuran da ta yi musu.

Related posts

Leave a Comment