Rahotannin dake shigo mana daga daga jihar Kano na bayyana cewar Kotun ?oli ta kori ?arar da ?angaren tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ya shigar yana ?alubalantar hukuncin da Kotun ?aukaka ?ara akan shugabancin APC a jihar.
?angaren Shekarau na korafi akan cewa za?en shugabannin jam’iyar da tsagin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ba sahihi ba ne.
Rahotanni sun bayyana cewar Kotun ?olin a ranar Juma’a, ta tabbatar da hukuncin da Kotun ?aukaka ?ara da ke Abuja ta yanke, wanda ta tabbatar da sahihancin zaben shugabanni da bangaren Ganduje ya yi, inda Abdullahi Abbas ya zama shugaban jam’iyar APC na Jihar Kano.
