Ministan harkar noma da cigaban kauyuka, Alhajj Sabo Nanono yabada dalilan da suka sa har yanzu mai yasa Najeriya take kamfar abinci bayan kuma tana samar da wada taccen abinci acikin kasar.
Alhaji Sabo Nanono ya fadi hakanne kwanan nan yayin da yake kokarin ciyar da kasar gaba, yace ahalin da ake ciki yanzu Najeriya bata da isassun kudin da zata sayo abinci zuwa cikin kasar nan.
Sannan ya alakanta hakan da rashin aikin yi wanda shine yake hana mutane samun kudin da zasu sayi abincin da zasuci, su biya haya da kudin ilimin ‘ya’yansu, wannan shine babban kalu balen da kasar nan take fuskanta ahalin yanzu.
“Yakara da cewa akwanan nan na hadu da wasu matasa ‘yan Najeriya da suke kokarin hada hannu da harkar noma da masana’antu, inda yace irin abinda ake da bukata kenan a cikin kasar, sai dai idan mun samar da dangantaka mai karfi atsakanin su dan yakar talauci.
Nanono yace gwamnatin tarayya zata cigaba da samar da sabbin dabaru wajen tai makawa dan samar da cigaba ga harkar noma dan karfafa darajar noman kamar yadda kasar china sukeyi.
Kazalika ya kara da cewa zasu ciyar da harkar noma gaba acikin kasa dan samun nasarar kalubaken da suke fuskanta na karancin samar da ingan taccen abinci ga masu yin bara, da tamowar yinwa da rashin wurin inganta abinci ya daina lalacewa.
“Wannan tana daga cikin halayyar talakawan duniya musamman ma ‘yan Najeriya mazauna kauyuka da basa maida hankali akan adana abinci.
