Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato na bayyana cewar Majalisar Malaman addinai a jihar ta yi Alla-wadai da kashe-kashe da asarar gonaki, gidaje da sauran dukiyoyi dake faruwa a wasu sassan jihar kwanakin nan.
Majalisar a jawabin da ta saki ranar Juma’a a Jos kuma shugabanninta Pandang Yamsat da Muhammadu Haruna, suka rattafa hannu, sunce wannan kashe-kashe ya saba dokokin Allah, kuma ya ci karo da ‘yancin rayuwa ta bil adama.
A cewar majalisar, wannan abu dake faruwa ya sabawa koyarwan addinin Musulunci da na Kirista. Kashe-kashen dake faruwa a Plateau ya saba dokokin Allah, inda Malaman addinai suka yi kiran jama’a suji tsoron gamuwarsu da Ubangiji.
“Majalisar IRC wacce ta kunshi shugabannin Kirista da Musulunci a jihar Plateau sun yi Alla-wadai da bayyana fushinsu kan kashe-kashe, kone-konen gidaje da gonaki dake faruwa a Bassa, Riyon da Barkin Ladi.”
“Wannan kashe-kashe gaba daya sun sabawa dokokin addinin Musulunci da Kirista; sun sabawa dokokin Allah kuma rashin tausayi ne. Kuma hakan na da hadari ga rayuka, abinci da tattalin arzikin jihar da kasar ga baki daya.”
“A matsayinmu na Malaman addini, muna kira ga dukkan wadanda ke da hannu cikin wannan abu su sauya tunani kuma su tattauna da juna kamar da littafai addinai suka koyar.” Majalisar ta yi kira da gwamnati da jami’an tsaro su tsaurara matakan tsaro domin kawo karshen matsalar a jihar.
