Labari mai dadi da ke bayyana a masana’antar Kannywood shi ne batun auren fitacciyar jaruma Aisha Aliyu Tsamiya. Majiyoyi masu yawa sun tabbatar da cewa za a daura auren a ranar Juma’a.
Shafin Labaran Kannywood na Twitter ya fara wallafa labarin amma sai dai sun sanar da cewa jita-jita ce babu tabbaci. “Mun samu jita-jitar cewa a ranar Juma’ar nan mai zuwa jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce… Kuma angon nata babban mutum ne.”
A karon farko, mun ci karo da wallafar jarumi Ali Nuhu inda ya saka hoton jarumar tare da yi mata fatan alheri. Ya ce: “Allah yasa alheri daughter” Baya ga nan mun ci karo da wallafar tsohuwar jarumar masana’antar, Zahrau Shata, inda ta saka hoton Aisha Tsamiya sannan ta rubuta: “Allah ya sanya alkhairi kanwata.”
“Za a yi bikin Aisha Aliyu Tsamiya, ranar Juma’a 25 ga watan Fabrairu a masallacin Sheikh Salban, kwanan ‘yan wanki kusa da gidan Tanko Yakasai. Muna rokon Allah yasa albarka kuma ya basu zaman lafiya. Amin ya Allah.
