EFCC Ta Dira Kan Kadarorin Tsohon Gwamnan Imo

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci cewa a raba Rochas Anayo Okorocha da wasu gidajensa da su ke birnin Abuja.

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta tabbatar da wannan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a yammacin ranar Alhamis.

Mai magana da yawun EFCC na kasa, Wilson Uwujaren ya bayyana cewa su na zargin da dukiyar haram Rochas Okorocha ya mallaki wannan gidan. Kamar yadda hukumar ta bayyana, za a raba tsohon gwamnan na jihar Imo da wannan kadara ne har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar da ake yi da shi.

Gidan talabijin na Channels TV ta rahoto cewa Alkali Emeka Nwite ya zartar da wannan hukunci a zaman da ya yi a ranar Alhamis, 24 ga watan Fubrairu 2022.

Related posts

Leave a Comment