Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Ibrahim Babangida ya ce ya fi Shugaba Muhamamdu Buhari da sauran shugabannin dimokuradiyar ?asar ya?i da rashawa.
Tsohon sugaban ya shaida hakan ne a lokacin wata hira ta musamman da tashar ARISE TV a wannan Juma’ar.
Ya kuma ce mutanen da suka yi aiki a ?arkashinsa mutanen kirki ne sama da wanda ake gani yanzu haka a mulki.
Shugaban na mulkin soja ya ce yayinda ya ya?i tsohon gwamnan mulkin soja da ya wawushe N313,000, mutanen da suka sace biliyoyi na tafiya a yanzu cikin ?anci.
Da aka tambaye shi cewa ko ya amince cewa rashawa ta yawaita a lokacin mulkinsa, IBB ya mayar da martani cewa, “ba abu ne da za a iya kwatantawa da wanda ake gani yanzu a zahiri ba.
“Daga abin da na karanta, da kuma sharhi, ina ganin mu tsarkakakku ne idan aka kwatanta da abin da ke faruwa a yanzu karkashin mulkin dimokuradiya.
“Na kori gwamna kan sata da almubazaranci kan kasa da N313,000 amma a yau, mutanen da suka wawushe bilyoyi har maganarsu na kotu na tafiya hankali kwance a titi. Don haka wane ne ya fi ya?ar rashawa?”
IBB yana da kyakyawan ala?a da shugaba Buhari, da ?aura alhakin sa?anin da ake ganin akwai tsakaninsu kan kofofin yada labarai
