Rahotanni daga Fadar Sarkin Musulmi Mai Alfarma Sa’ad Abubakar III na bayyana cewar Sarkin ya umarci al’ummar Musulmin ?asar su fara duba jaririn watan Muharram na shekarar Hijira ta 1443 ranar Lahadi.
Mai alfarmar ya bayar da umarnin ne a ranar Asabar cikin wata sanarwa da shugaban kwamatin shawarwari na Masarautar Sokoto Farfesa Sambo Junaidu ya sanya wa hannu.
“Ana sanar da al’ummar Musulmi cewa Lahadi 8 ga watan Agusta wadda ta yi daidai da 29 ga watan Zul-Hijja 1442 AH, ita ce ranar da za a fara duba sabon watan Muharram na 1443 AH,” a cewar sanarwar.
Sarkin ya yi addu’ar Allah ya agaza wa Musulmai wajen aiwatar da ayyukan ibadarsu.
Ganin watan Muharram wanda shi ne watan farko a kalandar Musulunci, shi ne zai bai wa Musulmai damar shiga sabuwar shekara ta 1443 bayan hijirar Annabi Muhammadu SAW daga garin Makka zuwa Madina.
