Boko Haram: Na Yi Alkawarin Kai Kukan ‘Yan Arewa Ga Buhari – Pantami

Ministan Sadarwa da tattalin arzi?in fasahar yanar gizo, Dr Isa Ali Pantami ya ce zai mi?a sa?wannin jama’ar Arewa ga Shugaban ?asa Muhammad Buhari bisa kisan gillar da ?an Boko Haram suka yi na manoma 43 a jihar Borno.

A ranar asabar, ne rahotanni suka bayyana cewa ?an Boko Haram sun shiga ?auyen Zabarmari, dake ?aramar hukumar Jere, jihar Borno, sun bi manoma har gonakinsu sun yi musu yankan rago.

Sheik Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na sadarwarsa a manhajar Tuwita bayan wani mai amfani da shafin ya ro?e shi da yin hakan.

Wanda yayi ro?on mai suna Boss Mustapha@__yellows) ya rubuta kamar haka. Don Allah don Annabi ka samu ka yi ma shugaban ?asa magana. Mutum arba’in da uku (43), ko a fim aka kashe wannan adadi lokaci daya, abun zai bada tsoro.
“Don Allah a taimaka a yi wani abun a kai, abun ya fara yawa #ZabarmariMassacre”.

Shi kuma Pantami sai ya mayar masa da martani cikin harshen turanci kamar haka. “Muna ta yin hakan, kuma zamu cigaba da yin hakan In sha Allah. “Shi ma zan yi masa magana kamar yadda nayi magana da gwamna Zulum ?azun nan. “Allah ya ji?ansu, ya kuma kawo mana ?arshen wannan bala’in”.

Arewacin Najeriya dai na fama da matsanancin matsalar rashin tsaro da ta ha?ar da Boko Haram, ?an bindiga, ?an fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Rahotanni daga ?ididdigar baya bayan nan sun nuna cewa an yi garkuwa da fiye da mutane 1,500 a arewacin Najeriya baya ga biyan ?imbin ku?a?en fansa.

Kazalika, rahotanni sun nuna cewa a?alla mutane 36,000 rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukansu tun daga shekarar 2009, da ?ungiyar ta ?ulla, zuwa yanzu.

Kazalika ayyukan ?ungiyar sun tilastawa sama da mutum miliyan biyu barin muhallansu, inda ?an Najeriya 240,000 suka yi gudun hijira zuwa ma?wabtan ?asashe.

Related posts

Leave a Comment