Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe za?en fitar da gwani na ?an takarar shugaban ?asa a jam’iyyar PDP.
Atiku ya lashe za?en ne bayan da ya samu jimillar ?uri’a 371. Ya kayar da gwamnan Rivers Nyesom Wike wanda ya zo na biyu da ?uri’a 237.
Kafin fara za?en ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwar ya sanar da janye wa Atiku, tare da umartar dukkan wa?anda za su za?e shi su mara wa Atiku baya.
?uri’ar da kowanne ?an takara ya samu
Tariela Oliver 1
Sam Ohabunwa 1
Pius Anyim 14
Udom Emmanuel 38
Bala Mohammed 20
Bukola Saraki 70
Nyesom Wike 237
Atiku Abubakar 371
Ayo Fayose 0
Dele Momodu O
Charles Ugwu 0
Chukwendu Kalu 0
Ba wannan ne farau ba
A shekarar 2019 ma Atiku ya yi wa PDP takara, amma ya yi rashin nasara a babban za?e, wanda shugaba Muhammadu Buhari mai ci ya lashe.
A yanzu ?an shekaru 75 ?in zai fuskanci duk wanda APC za ta tsayar a nata za?en da za ta yi a ranakun shida da bakwai na watan Yuni.
Wannan ne karo na shida da Atiku Abubakar ke yin takarar shugaban ?asa ba tare da ya samun nasara ba.
