Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya ce zai goyi bayan duk wanda ya yi nasara a za?en fitar da gwani na ?an takarar shugaban ?asa a jam’iyyar PDP.
Wike shi ne ?an takara na ?arshe wanda ya yi jawabi ga wakilan PDP da za su fitar da gwani tsakanin masu son takarar shugaban ?asa a jam’iyyar.
A cikin jawabinsa ya ce PDP na bu?atar irinsa domin kawar da APC daga mulki
