Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya ja hankalin Ya’yan jam’iyar APC a jihar da cewa su cigaba da hada kansu da kuma yin aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyar a zaben shekara ta 2023.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya wanda yayi jan hankalin a lokacin da yake jawabi a wurin zaben fidda gwani na sanata na mazabar Gombe ta tsakiya da tsohon gwamnan jihar Sanata Muhammad Danjuma Goje ya lashe.
Gwamnan yace hadin kai na ya’yan jam’ iyar yana da matukar muhimmanci saboda hakan zai kai jam’iyyar ga samun nasaraa zaben gama gari na shekara ta 2023.
Ya kuma bayyana farin cikinshi bisa yadda yadda zaben fidda gwani na jamiyar ta APC a jihar Gombe ya gudana, yana mai kuma yabawa da yadda ?a?an jamiyar suka gudanar da kansu cikin tsanaki.
A jawabin Sanata Muhammad Danjuma Goje wanda wannan ne karo na hudu da ya yi takarar sanata na mazabar Gombe ta tsakiya, yace zai hada kai da dukkannin ‘yan takara suyi aiki tare wurin ya?in neman zabe domin nasarar jam’iyar APC a jihar Gombe.
Sanata Muhammad Danjuma Goje ya bayyana farin ciki ga wakilai wato delagates saboda zabarshi da suka yi, inda ya kara da cewa bazai watsa musu kasa a ido ba domin zai jajirce wurin tabbatar da samar da ribar dimokradiya ga al-ummar mazabar shi .
