2023: Dogara Ne Mafi Cancanta Da Zama Mataimakin Tinubu – Matasan APC

Daga Adamu Shehu BAUCHI

Kungiyar matasan arewa karkashin Jam’iyyar APC a arewacin Najeriya sunce babu wani wanda ya dace da kujerar mataimakin Shugaban kasa kaman tsohon kakakin majalisar tarayya Honorabul Yakubu Dogara daga Arewacin kasan nan domin samun daidaito tsakanin manyan addinai guda biyu na Musulunci da Kiristiyaniti.

Shugaban Kungiyar na ?asa Ukkasha Hamza ya fadi hakan a zantawarshi da manema labarai a Bauchi.

Matasan sun kara da cewa biyo bayan lashe zaben fidda gwani na ?an takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulkin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi, suka gamsu za?o Yakubu Dogara a matsayin mataimakin sa hakan zai cire wani shakku da zargi a zukatan ‘yan Najeriya na sake zaben APC don cigaba da mulkin kasan a zaben 2023.

Har-ila yau sunyi nuni da cewa a kasa irin Najeriya dake cike da al’adu dabam dabam da addinai a cewarsu ya kamata ?an takarar ya zama daga ?angaren Kiristoci ne daga arewacin kasan domin adalci da kuma kawo zaman lafiya ga Jam’iyyar APC da kuma nuna ana tare da kowa a siyasance.

Bugu da Kari suka ce bayan maganar addini Yakubu Dogara dan siyasa ne na gari wanda yake da jama’a a dukkanin fadin Najeriya kasancewarshi tsohon Shugaban majalisar tarayya, hakan ya bashi daman kwarewa ta fannin shugabanci musamman a siyasance.

Related posts

Leave a Comment