2023: Najeriya Na Bukatar Jajirtaccen Shugaban Kasa – Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, ya lissafa wasu muhimman abubuwa da ya zama dole shugaban kasa na gaba ya duba su.

A ruwaito yayin jawabin da Obasanjo ya yi a wani taro da aka yi ta kafar intanet da Africa Leadership Group ta shirya, ya ce dole shugaba na gaba ya magance manyan kallubalen da kasar ke fuskanta bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya kara da cewa dole shugaba na gaba ya kawo karshen kalubale da ?asar ke fama dasu kamar ta’addanci, yan bindiga, da garkuwa da mutane a jihohin kasar.

Obasanjo ya ce dole Najeriya a matsayinta na kasa ta yi kokarin wuce matakin tunani kawai ta zama mai aiwatarwa domin cimma wannan nasarorin. “Ina fatan mutumin da zai zama shugaban kasa na gaba, zai zama irin shugaba ne wanda zai fahimci tattalin arziki, wannan na da muhimmanci.

“Idan ya fahimci tattalin arziki, akwai abubuwa da ya zama dole ya yi; yin wani abu kan tallafin man fetur. Kuma, bashin kasar bai da kyau, dole a yi wani abu kansa. “Adadin man fetur da ake sacewa a kasar abu ne mai daure kai. Rashawa da ake yi a wasu sassan shima abin damuwa ne. Kuma, yan bindiga, da garkuwa sun zama ruwan dare.”

Related posts

Leave a Comment