Daga Adamu Shehu Bauchi
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi ya ja hankalin shugabannin Addinai da su cigaba da yi wa Jihar Bauchi da Najeriya baki daya addu’a musamman yanzu da kasar ke tunkarar manyan zabubbuka na shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen taron addu’oi na musamman da hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar ta shirya a sansanin Alhazai na din-din-din dab da filin tashin jiragen sama na kasa da kasa da ya gudana a ranar Jumma’a.
Bala yace, “ku dukufa wajen yi ma Jihar mu ta Bauchi addu’a, zaben 2023 Yana karatowa ga kuma ‘Yan takara bila adadin wadanda suka nuna sha’awarsu akan kujera daya suna nan da yawa, wannan baya rasa nasaba da irin ayyukan da muka faro da ci gaba mai dorewa, za ku gani mutum goma suna neman kujera daya a jamiyya daya.
Yace, ga kuma yan wasu jamiyyar su ma suna nema, saboda haka Addu’o’in ku zai sa dan takarar na gari ya samu ya fito domin muyi ma mutane aiki sosai babu kama hannun yaro”. Gwamnan ya jaddada
Gwamnan ya kara da cewa, “ku ba yan siyasa bane kuyi mana addu’a domin dan’takara na gari ya samu ya fito, wanda yake da zuciya da zai taimaki al’umma, kana mu hada hannu domin kawo mana ci gaba a Jihar baki daya”.
Kana yace in aka ba wadanda suka cancanta, to daga karshe za asamu zaman lafiya mai dorewa , don haka mutane su lura wajen zaben Yan takara na gari.
“Ba don ni kadai ba, jama’ar Bauchi ne a gabanmu saboda haka wadanda ake ganin zasu yima mutane aiki tukuru su za’a tsayar su fafata a zaben dake tafe, musamman tsakanin ‘yan majalisun jihohi da na tarayya da kuma na Gwamna”.
