Gwamnatin tarayya ta samu nasara a kotun Allah ya isa kan iyalan marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, bisa zargin da ake musu na hannu cikin wawuran kudin kasa da mahaifinsu yayi.
Gwamnati na son kwato wasu makudan miliyoyi da ake zargin marigayin ya boye a wasu kasashe irinsu Amurka da Birtaniya da sauran Manyan ?asashen duniya.
Kotun koli a ranar Juma’a, 13 ga Junairu, ta yi watsi da daukaka karar da iyalan marigayi Abacha suka shigar inda suka bukaci kotun ta hana gwamnati bude takardun bincike kan mahaifinsu da wasu iyalansa da ake zargi da hannu.
Hukuncin kotun Alkalan kotun karkashin jagorancin Alkali Emmanuel Agim, sun yi ittifakin cewa bincike ya nuna babu gaskiya cikin bukatar da iyalan Abacha sukayi. Saboda haka ya yi watsi da karar kuma hakan ya bawa gwamnatin daman cigaba da tuhumarsu.
