Za Ka Gane Kurenka Idan Ka Yi Gigin Murde Mana Zabe – Kwankwaso Ga Ganduje

‘Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace duk wanda yayi zagon kasa garesa a Kano a zaben shugaban kasa da ke zuwa zai yi nadama,

An ruwaito ganduje a baya-bayan nan ya sanar da magoya bayansa da ke jihar cewa, Kano za ta maimaita abinda ya faru a zaben shugaban kasa na 1993 lokacin da suka goyi bayan ‘dan takarar kudu (marigayi MKO Abiola) tare da yin watsi da na jiharsu (marigayi Bashir Tofa), a kokarinsa na cewa za a zabi Tinubu a bar Kwankwaso.

Amma a yayin martani bayan kwanaki, Kwankwaso yace: “Babu dadewa na yi rali wanda ya kasance mafi kyau. Na yi daya a Wudil, kudancin jihar, na yi daya a Bichi, arewacin jihar.

“Na bude ofishina a Kano ta tsakiya kuma rali mafi kyau da nayi mafi kyau saboda ba a gwada shi da irin na wasu ‘yan takara da suka tara taron jama’ar da suka zo daga wajen jihar.” “Yanzu ka gani, ba na son batun wannan mutumin. Ban san ko yace ko bai ce ba, amma batun gaskiya shi ne, duk wanda yayi zagon kasa ga NNPP ko Kwankwaso a 2023, wata rana zai yi nadama kan kuskuren da ya tafka.

“Duk wanda ya san ni, ya san abinda na yarda da shi, idan na ci zaben shugaban kasa, Kano za ta fi ko ina mora, arewacin Najeriya da kasar baki daya.

‘Toh ina mamaki idan ka je kana cewa in yi rali, rali dai na yi su da yawa a Kano. A cikin watannin Janairu da Disamba a Kano, na je yankuna uku na jihar, toh mene ne matsalar ka da yin rali na a Kano?”

Related posts

Leave a Comment