2023: Masana Sun Gargadi Wike Kan Goyon Bayan Atiku

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban daraktan gidan rediyon Muryar Najeriya VON, Osita Okechukwu ya shawarci gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da kada ya kuskura ya mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya.

A ‘yan kwanakin nan gwamna Wike na ganawa da jiga-jigan siyasar Najeriya a jam’iyyu mabambanta, lamarin da ke kara kada hantar Atiku.

A ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta ne gwamnan ya gana da dan takarar shugaban ?asa na APC, Bola Tinubu da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour a birnin Landan.

Haka nan, ya gana da tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo duk dai a birnin na Landan tare da wasu jiga-jigan Siyasar Najeriya.

Da yake tsokaci game da makomar siyasar Wike, Okechukwu ya gargadi gwamnan da kada ya bari ya kassara a harkokin siyasa a kasar nan, ya ce a yanzu dai gwamnan na jihar Ribas na more yadda harkokinsa ke tafiya, don haka ne ma yake jan hankalin jiga-jigan siyasa da dama.

Shugaban na VON ya shawarci gwamna Wike da ya yi biris da batun Atiku bisa zargin yaudararsa (Wike) da ma yankin kudu. A cewar Osita: “Shawarata ita ce, kada ya kuskura ya sakawa Atiku Abubukar da alheri, ganin yadda ya ci amanar Kudu da shi kansa Wike din, wanda shi ya cancanta ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a PDP.”

A ganin Okechukwu, kamata ya yi a ce Wike ya koma tsagin Tinubu ko kuma Peter Obi, ya kafa hujja da ganin yadda APC ke da dan takara mai kwarin gwiwa da karbuwa, da kuma LP mai dan takarar da ke da jama’ar da ke kaunarsa a yankinsu. Ya kuma ce, har ‘yan Arewa ba sa farin ciki da yadda Atiku ya yaudari ‘yan yankin Kudu a zaben fidda gwanin da aka kammala.

Related posts

Leave a Comment