Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Jam’iyyar APC ta reshen jihar, ta nesanta kanta daga zargin rufe wani gini da aka maida ya zama hedikwatar jam’iyyar NNPP a Maiduguri.
A wani jawabi da ya fito daga shugaban APC a Borno, Ali Bukar Dalori yace ba da hannunsu aka rufe ofishin NNPP ba, Hakazalika gwamna Babagana Zulum bai da masaniya.
Hon. Ali Bukar Dalori yake cewa jam’iyyar APC tayi mamakin jin NNPP na zarginta ko Gwamnan Borno da bada umarnin garkame mata sakatariya a jiya. Babu ruwan APC – Hon. Ali Bukar Dalori “Hankalinmu ya zo ga wani zargi mara tushe da ake yi wa APC ta Borno da Mai girma Babagana Zulum na rufe sakatariyar NNPP a Maiduguri.”
Mazauna unguwar da wannan ofishi yake na Abbaganaram sun koka a kan yadda su Hon. Attom Tom suka kafa sakatariyar siyasa a tsakiyar gidajensu.
