Mohamed Salah ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Liverpool kaka uku.
Saura kaka daya kwantiragin dan wasan mai shekara 30 dan kwallon tawagar Masar ya kare a Anfield, daga baya aka kama rade-rade kan makomarsa a Liverpool.
Salah ya ci kwallo 156 a wasa 256 da ya yi wa Liverpool a kaka biyar da ya yi a Anfield, tun bayan da ya koma kungiyar daga Roma.
An fahimci cewar sabuwar yarjejejeniyar da Salah ya kulla ya zama dan kwallon da zai ke karbar albashi mafi tsoka a tarihin kungiyar.
Salah ya lashe Champions League da Premier League da FA Cup da League Cup da Fifa Club World Cup da kuma Uefa Super Cup a kungiyar Anfield.
Haka kuma ya lashe takalmin zinare uku a Premier League da ake kira Golden Boots, an kuma zabi dan wasan karo uku a PFA player of the year karo biyu tare da Klopp.
Wannan sa hannu da Salah ya yi zai kara karfafa gwiwar magoya bayan Liverpool, bayan da Sadio Mane ya koma Bayern Munich a bana.