Siyasa: Atiku Ya Gana Da Wike A Birnin Landan

Labarin dake shigo mana daga birnin Landan na ?asar Ingila na bayyana cewar ganawar da aka jima ana dakon gani tsakanin ?an takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da Gwamna Nyesom Wike, ya gudana daga ?arshe a birnin Landan.

An ruwaito cewa har yanzu ba’a bayyana cikakken bayanin abin da taron jiga-jigan PDP biyu suka tattauna a taron ba, wanda ya gudana jiyaa ranar Laraba.

Amma wasu bayanai sun ce ganawar ta maida hankali kan lalubo hanyar sulhu a tsakanin su da kuma bukatar cigaban jam’iyyar PDP zuwa mataki na gaba.

Wa?anda suka halarci taron ganawar Atiku da Gwamna Wike sun ha?a da gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da takwaran su na jihar Benuwai, Samuel Ortom.

Tsohon mataimakin shugaban ?asa, Atiku ya shiga taron ganawar tare da rakiyar gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri. Awanni ka?an bayan tsohon shugaban ?asa, Chief Olusegun Obasanjo, da ?an takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, sun gana da Wike.

Related posts

Leave a Comment