2023: Magoya Bayan Atiku Sun Juya Baya

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar mai suna “Atiku State of Mind” ta janye goyon bayanta ga dan takarar na shugaban kasa a PDP ta koma goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Mr Kingsley Moghalu a zaben dake tafe na 2023.

An ruwaito Mr Hassan Ankuma, tsohon shugaban kungiyar na kasa, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin taron manema labarai da ya kira don goyon bayan dan takarar na ADC a Abuja.

Ankuma ya ce kungiyar ta yi kurakurai a baya ta hanyar goyon bayan yan takara daga manyan jam’iyyu biyu da ke Najeriya kadai wanda hakan ya haifar musu da matsala, amma a yanzu hakan ba zai sake faruwa ba.

“Kuskuren da muka yi a baya shine ‘yan takara daga manyan jam’iyyun siyasa biyu na kasar nan muke goyon baya tamkar su kadai ne yan takara. Dogaro kan wadannan manyan jam’iyyun biyu ne yasa muka rika zaben shugabanni marasa nagarta su kadai muke zaba ko da wadanda suka tsayar ba su da nagarta”.

“A yau, muna da mambobi daga jihohin Ribas zuwa Borno da Sokoto da sauran jihohi domin fara sabuwar tafiya ta kawo sauyi. “Ni da tawaga ta mun sauya daga kungiya ta goyon bayan Atiku mai suna “Atiku State of Mind” zuwa “Moghalu State of Mind”.

“Muna son kasa mai inganci da zaman lafiya wacce za ta tabbatar an cika wa mutane alkawurran da aka dauka yayin yakin neman zabe. “Ba mu son shugaba da zai rika tunanin kasaitarsa ce ta sa aka zabe,” in ji Ankuma.

Related posts

Leave a Comment