Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum na cigaba da ba talakawan jihar tallafin azumi domin saukaka musu wahalar rayuwa.
Gwamnan ya ?auki wannan matakin ne sa?anin wasu jahohi da ake ba shugabannin ‘yan siyasa kawai saboda manufar siyasa.
Gwamna Zulum ya ziyarci karamar hukumar Mungono tun ranar Alhamis inda ya raba kaya abinci da na sawa na kimanin miliyan ?ari biyu da saba’in 270m a karamar hukumar.
Kimanin maza da mata dubu casa’in 90:000 ne suka amfana da tallafin kayan abinci dana sanyawa a lokacin wannan wata mai alfarma na Ramadan.
