2023: Karbar Mulki Ne Mafita Ga PDP – Atiku

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon Mataimakin Shugaban ?asa kuma Atiku Abubakar, ya shawarci Kwamitin Dattawa da Amintattun PDP su ha?a kai su tabbatar cewa PDP ta yi nasara a za?en 2023.

Atiku ya yi masu wannan kira ne a taron ganawar da ya yi da su ranar Talata a Abuja, inda ya nemi goyon bayan su don ganin an tsaida shi takarar shugaban ?asa a ?ar?ashin PDP, a za?en 2023 mai zuwa.

Ya ce za?en 2023 ya bai wa PDP damammaki masu yawa na samun nasara kuma jam’iyyar ta koma kan mulki.

“Amma kuma na damu sosai cewa idan ba mu ha?a kai muka ci za?en 2023 ba, to kenan fa za mu sake jiran yin adawar shekaru takwas kenan.

“Nan da shekara takwas kuwa ban san iyar wa?anda za su yi bankwana da siyasa ba. Sannan kuma hakan zai iya kashe jam’iyyar.

“Don haka wannan lokaci ne mai matu?ar muhimmanci ga ci gaban rayuwar mu baki ?aya. Ina so ku ?ara zama da natsuwa ku yi karatun ta-natsu.

Related posts

Leave a Comment