Rahotannin daga birnin Landan na bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya bukaci gwamnonin APC su bar gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban gwamnonin Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
Hakan na faruwa ne a yayin da Shugaba Buhari ya gana da Mai Mala Buni a birnin Landan ranar Talata.
Buhari ya ce ya fahimci rigimar da ke faruwa a cikin jam’iyyar lamarin da ya sa aka kai kara kotu, yana mai cewa duk da haka ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin babban taron jam’iyyar da ake shirin gudanarwa ranar 26 ga watan Maris.
Buhari ya bukaci a guje wa abubuwan da za su dagula jam’iyyar yana mai cewa “da farko batun shugabancin riko na jam’iyya zai komo kamar yadda yake a baya.
Shugabancin APC ya shiga ru?ani ne a ?arshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasi?a ta ?ulla cewa Mai Mala ne ya ba shi ri?o saboda ya yi tafiya ?asar waje don a duba lafiyarsa.
Rikicin shugabanci a APC ya ?ara ?amari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020.
