2023: Hamza Al-Mustafa Ne Mafita A Najeriya – Matasan Najeriya

A daidai lokacin da kakar za?e ta Shekarar 2023 ke ?ara ?aratowa gamayyar ?ungiyoyin Matasan Najeriya sun yi ittifa?i akan cewa mutum guda da zai iya kai kasar ga tudun mun tsira shi ne tsohon dogarin tsohon shugaban kasa Abacha wato Hamza Al-Mustafa.

Da yake ba da tabbaci akan haka shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Najeriya Alhaji Abdullahi Abubakar Wali a ganawar da ya yi da manema labarai a Kaduna ya ce, halin da Najeriya ta tsinci kanta yanzu a ciki Mutum irin Hamza Al-Mustafa ne zai iya ceto ?asar daga wargajewa.

Matasan sun bada misali da irin kwazo da nasarorin da Hamza Al-Mustafa suka samu a zamanin mulkin Abacha inda suka yi kira da babbar murya ga dukkanin ‘yan Najeriya da su mara wa tafiyar Hamza Al-Mustafa baya domin kai wa ga nasara.

Abubakar Wali ya ba da misali da Irin kiraye-kirayen da maluman addini suke ta yi a wannan lokaci ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da batun jam’iyya su za?i cancanta kuma su yi fatali da batun tsofaffi wa?anda sun buga ba za su iya komai ba su za?i Matasa masu kishi, inda yace babu wanda ya dace da wannan hasashe sai Manjo Hamza Al-Mustafa mai ritaya.

Related posts

Leave a Comment