Duk da Ikrarinsa na yanke Hukuncin shiga takararar shugabancin kasa a cikin kwanaki ashirin da daya 21 da yayi alkawari, Gwamna Bala har yanzu ya gagara fitowa fili don bayyana ra’ayinsa kan wan nan batu na takarar Shugaban kasa a zaben gama gari na 2023 dake tafe.
In ba amanta ba ranar Alhamis shabiyu 12 ga watan ogusta na shekaran 2021 Gwamna yayi alkawarin zai bayyana ma magoya bayansa da masu ruwa da tsaki a niyyarsa da alkiblar sa na takarar a zaben 2023 amma shiru, kamar an aiki bawa garinsu.
Bala tun a farkon al’amaari, yace yana ci gaba da tuntubar abukan siyasar shi da suka hada da gwamnonin da Yan majalisar tarayya da ministochi, masu ruwa da tsaki a fadin Jihar Bauchi musamman shuwaganin Jam’iyyar sa ta PDP.
Gwamnan ya jaddada hakan ne a daidai lokacin da kungiyar matasan arewa maso gabas, Kungiyar matasa ta kasa reshen jijar Bauchi da Kungiyar aikin sufurin motocin haya (NURTW) reshen Jihar da Kuma Kungiyar yan’kasuwa da masana’antu na hannu, sukayi masa tattaki don nuna goyon bayansu akan ya fito takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023.
Kungiyoyin dai sun tabbatar ma da gwamnan Bauchi Bala Mohammed goyon bayansu dari bisa dari, inda yace su bashi sati uku, zai bayyana masu ko zaiyi takarar ko kuma akasin hakan, bayan ya gama tun tubar masu ruwa da tsakin a kasa baki daya.
Bala yace,” kuyi hakuri da yaddan Allah zan sanar da ku a cikin sati biyu ko sati uku, zan baku cikkakiyar amsar tambayar ku ko zanyi takarar shugaban kasa ko bazan yi ba” Yayi alkawari.
Bayan cikar sati uku, kwanaki ashirin da daya har da doriya, Gwamna Bala ya kasa fadawa magoya bayansa ra’ayinsa kan batun takarar,sai cewa yayi a Kara bashi wani karin sati ukun, har ila yau, yace ya lura Uwar jamiyyarsa a matakin Jihar tuni sun amince masa da ya fito, sauran gwamnonin, ministochi, duk sun bashi damar ya fito ya gwada, amma shiru kake ji
A cewar sa yana bukatar lokaci sosai tare da yin nazari kafin ya fito ya fadi alkiblarsa ga masu goya masa baya kan batun takarar,yace Najeriya tafi karfin mutum.daya ko yan’kalilan donnyanke hukunci, kan neman kujerar mulkin Najeriya, ko kuma zai Kanye batun ya sake Neman kujerar Gwamna a dubu biyu da ashirin da ukun 2023.
Wakilin Muryar Yanci’ yayi dubi kan wan nan alkawari, inda wan nan lahadin da ta wuce sha biyu 12 ga watan satumba 2021 itace karshen wa’adin da ya dauka zai bayyana tafiyarsa a siyasance, kimanin wata daya kenan, har yanzu babu labarin ko zaiyi ko ba zai yi ba
Daga Adamu Shehu Bauchi
