‘Yan Bindiga Sun Sanar Mini Luguden Wutar Da Ake Yi Bai Shafar Su – Gumi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Sanannen malamin addinin Islama mazaunin Kaduna, ya kara tabbatar wa da jama’a cewa a koda yasuhe ya na samun damar tattaunawa da ‘yan fashin dajin da suka addabi arewacin Najeriya.

A takardar da malamin ya fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa gungun ‘yan bindiga sun sanar da shi cewa luguden ruwan wutan da sojin saman ke yi ba ya taba su, sai dai ya taba matansu da ‘ya’yansu, domin kuwa suna da salon kauce musu, Punch ta ruwaito.

Gumi ya ce ‘yan bindigan sun kware tare da zama ‘yan hannu wurin kauce wa duk wani bam da sojin sama za su wurgo, hakan ne yasa da kyar a iya kama su ko halaka su.

“Abinda ba dole ku sani ba shi ne, ‘yan bindigan sun kirkiro hanyoyin tsere wa luguden wuta ta sama. Sun sanar da mu cewa, za ku iya kashe matansu da ‘ya’yansu ne kawai ta wannan harin. “Abin nufi shi ne, idan aka matsanta musu a Zamfara, babu shakka za su sauya wuraren zama.

Toh dukkan Najeriya ce za ta kasance a wannan halin?

Gitaccen malamin ya bayyana cewa bayanai masu kyau, tsarin jami’ai nagari da kuma hada kai da makiyaya, sasanci duk suna cikin hanyoyin shawo kan matsalar ‘yan fashin daji.

Related posts

Leave a Comment