Tsaro A Kaduna: Sha’aban Ya Bukaci Musulmi Da Kirista Su Dauki Azumi

Mai girma ?an Buran Zazzau Alhaji Muhammad Sani Sha’aban ya yi kira da babbar murya ga jama’ar jihar musulmi da kirista cewa, kowa ya tashi da azumi a ranar Litinin mai zuwa domin kai kuka ga Allah ya kawo sauki dangane da matsalar tsaro dake addabar Jihar.

Sha’aban ya yi wannan kiran ne a wani muhimmin sako da ya aikewa jama’ar Jihar akan mawuyacin halin da Jihar ta tsinci kanta a ciki.

Basaraken wanda a hannu guda ya nemi takarar Kujerar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC, ya ce kiran ya zama wajibi duba da yadda jihar gaba daya ke cikin matsala ta tsaro.

Sani Sha’aban ya ?ara da cewar ba a yi za?en fidda gwani na takarar gwamna a APC a Jihar ba, kawai an aikata abin da aka ga dama ne ta hanyar ?auki ?ora, kuma tuni suka shigar da ?ara gaban kotu domin soke na?in da aka yi.

Related posts

Leave a Comment