Mashahurin Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani da su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, domin ciro masharin kukan su.
A cewar Malamin samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.
Dr Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.
Ya bukaci Fulani su hada kansu kada su bari ‘yan siyasa su raba su, yana mai cewa kabilarsu na da muhimmin rawa da za su taka wurin zaben shugaba na gari a Kaduna da ma Nigeria baki daya.
Dr Gumi ya yi wannan jawabin ne yayin mika kayan abinci da dabbobi ga iyalan Fulani wadanda rashin tsaro da annobar korona ta shafa wacce wata kungiya mai suna Bilital Marroobe Pastoralists Association of Nigeria (BILMPAN) ta shirya a Kaduna.
Ya ce, “Idan muna son kuri’un mu su yi tasiri, ya kamata mu hada kai wurin jefa kuri’un mu a zabe mai zuwa. Ya zama dole mu shirya yin aiki tare.”
Babban malamin ya kuma gargadi makiyayan musamman wadanda ke zaune a daji da su guji fashi da garkuwa da mutane. A cewarsa, karamcin da kungiyar makiyayan ta yi zai taimaka wajen rage wahalhalun da makiyayan ke fuskanta ba tare da jira sai gwamnati ta kawo musu dauki ba.
