Sojojin sama na Operation Thunder Strike sun kai hari a sansanin ?an bindiga a dajin Kuduru da Kuyambana. Sojojin ta hanyar amfani da jiragen ya?i sunyi nasarar halaka ?an bindiga da dama tare da lalata gine-ginensu Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce dakarun ta na Operation Thunder Strike sun kashe ?an bindiga masu yawa a harin da ta kai sansaninsu da ke dajin Kuduru da Kuyambana a jihar Kaduna.
” Kakakin rundunar ta musamman, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin rundunar na Twitter a ranar Juma’a a Abuja. Ya ce dakarun sojojin sun samu wannan nasarorin ne sakamakon hare-haren da suka kai a ranakun Laraba da Alhamis.
Enenche ya ce sojojin sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna yan ta’addan na amfani da wuraren don shirya kai hari kafin aka far musu. Ya ce an kai harin a ma?uyar ?an ta’addan a dajin Kuduru ne da na’urar le?en asiri daya nuna akwai ?an bindiga da dama a cikin gine-ginen da ke dajin.
“Jiragen ya?in sun yi ta ruwan bama-bamai ?aya bayan ?aya a inda gine-ginen suke inda suka kashe da dama tare da lalata sansanin.
“A dajin Kuyambana ne muka hango wasu ?an bindiga tare da shanu da suka sace kusa da wasu bukoki, jiragen NAF da jirage masu saukan ungulu sun musu ruwan wuta inda suka yi nasarar kashe mutane da dama cikin su,” in ji shi.
