Kungiyar dattawan Arewa ta gargadi kungiyar dattawan Neja Delta (PANDEF) kan barazanar da take yiwa Arewa kan lamarin wanda zai zama shugaban kasa a 2023.
Kungiyar ta yi raddi ne kan jawabin PANDEF na cewa Arewa ta jira sai 2031 kafin ta sake samun kujeran Shugaban kasa.
A jawabin da Kakakin PANDEF, Ken Robinson, ya saki, ya ce Arewa ta daina tunanin sake samun kujeran Shugaban kasa bayan mulkin Buhari.
Martani kan hakan, Kakakin Dattawan Najeriya, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya gargadi PANDEF da sauran kungiyoyin kudu cewa babu wanda ya isa ya yiwa Arewa barazana.
A hirarsa da DailyTrust ta ruwaito, yace: “Maganar gaskiya itace duk abinda PANDEF tace, hakkin kowane dan Najeriya ne zaben wanda yake so kuma wajibi ne a girmama hakkin jam’iyyun siyasa.”
“Arewa shirye take da ta zauna da kowa don tattauna yadda za’a yi, amma ba za’a cimma komai ta barazana ba, kuma muna jaddada cewa a daina yiwa Arewa barazana, babu wanda zai iya bamu tsoro.”
Baba-Ahmad ya yi kira ga kungiyoyin su mayar da hankali wajen samar da dan Najeriyan da ya cancanta kuma zai hada kan jama’a.
