“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tara taron jama’a ‘yan Najeriya fiye da fitattun ‘yan siyasa kamar su Azikiwe, Obafemi Awolowo da Aminu Kano, Duk da Awolowo, Azikiwe da Aminu Kano sun rasu, sun cigaba da samun mutuntawa da girmamawa a ko ina, amma ko ka?an ba su kama hannun Buhari ba”.
Wadannan Kalamai sun fito ne daga bakin mai magana da yawun Shugaban Kasa Mista Femi Adesina, a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.
A rubutun Adesina na wannan makon, mai magana da yawun Buhari ya daidaita da tunanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na cewa Buhari ne ya fi kowanne dan siyasa farin jini a tarihin Najeriya.
A takardar, Adesina ya rubuta cewa, “Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo mutum ne nagari. Duk abinda ya fadi, ku dauke shi da muhimmanci. “Akwai yuwuwar ka ce, toh me ake tsammanin mutum na biyu a kasa ya fadi game da shugabansa?
“Sai dai duk wanda ya yi aiki da Farfesa Yemi Osinbajo da Buhari, zai gane gaskiya. Mutum ne nagari kuma wanda ya dogara ga Ubangiji. Ba abun a mutu ko a yi rai ba ne, da ya zaba sai ya yi shiru game da halayen shugaban kasa.” Femi Adesina ya kara da cewa:
“Ina da shekarun da ya dace in ce na ga abubuwa da yawa da kuma lamurran siyasa masu yawa. Na ga zamanin Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe, Shehu Shagari, Aminu Kano, MKO Abiola, Bashir Tofa da sauransu.
“Amma ban taba ganin mutum mai irin jan hankali, daukar jama’a da farin jinin Muhammadu Buhari ba. A dukkan fadin kasar nan, arewa da kudu. Jama’a baibaye shi su ke kamar zuma.”
