Daso Ta Musanta Labarin Karbar Mota Daga Dubai


Wani labarin da ya cika kafar sadarwa na kyautar Mota da Gwamnatin kasar Dubai ta bai wa fitacciyar Jarumar Saratu Gidado ya zama kanun jarudu a ranar Alhamis wanda hakan ya sa wakilin Dimukaradiyya ya nemi jin gaskiyar maganar daga bakin Saratu Gidado, in da ta bayyana masa cewar.

“Su masu yada labarin ba su saurari maganar da na yi a shafuka na ba ne, domin babu in da na ce wani ko Gwamnatin kasar Dubai sun ba ni kyautar Mota, kuma su je shafin nawa su Kara dubawa sosai.” Inji ta.

Ni abin da na ce a shafin mun je Dubai mun shiga kanti mun yi sayayyar kayan tsaraba kuma za mu koma gida Nigeria, amma ban ce an ba ni kyautar Mota ba, kawai dai na rike wata Leda mai hoton Mota a jikin ta, amma ban ce an ba ni kyautar Mota. ” a cewar ta.

Daga karshe ta yi kira ga ‘yan jarida, da su rinka tantance labarai Kafi su yada shi.

Related posts

Leave a Comment