Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce ya kamata jam’iyyar APC ta tsayar da ?an yankin kudu a takarar shugaban ?asa idan ta na son cigaba da mulki a 2023.
A wani rubutu da gwamnan ya fitar a shafinsa na dandalin Facebook, Gwamna Akeredolu ya ce shi da ‘yan uwansa gwamnoni na kudancin Najeriya kar?ashin ?ungiyarsu sun cimma matsaya ?aya.
A cewarsa baki ?aya mambobin ?ungiyar gwamnonin kudu sun amince cewa ya zama wajibi mulkin ?asa ya koma hannun ?an yankin su. “Wajibi APC ta yi duk mai yiwuwa don cigaba da mulki, wajibi mu aiwatar da tsarin kar?a-kar?a matukar muna son cin nasara mu cigaba da mulki”.
APC ta shiga ru?ani tun bayan tsaida Atiku An yi ta ya?a jita-jitar cewa mai yuwuwa APC ta ba ?an arewa tikitin takara biyo bayan sakamakon zaben fidda gwanin PDP, wanda ya ba tsohon mataimakin shugaban ?asa, Atiku Abubakar, nasara.
