Badakala: Kyari Ya Fasa Kwai

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar dakataccen Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, ya yi zargin cewa matakin da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya dauka na mika shi Amurka, ba shi da amfani ga shari’a.

Kyari ya yi ?arin haske akan alakarsa da Hushpuppi a daya daga cikin sabbin kararrakin da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni.

Tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sandan, ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da kada ya amince da tasa keyar sa zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan hannu a wata damfara da ake zargin sa.

Ya yi zargin cewa shirin mika shi Amurka domin gurfanar da shi ba komai bane face nufin hukunta shi, da cin zarafin sa. Da yake bayyana cewa kama shi da tsare shi yana da wasu manufofin siyasa, babban jami’in ‘yan sandan ya yi ikirarin cewa mika shi zuwa kasar waje zai ?arfafa kungiyoyin laifuffuka daban-daban da tawagarsa ta IRT ke yi.

“A gaskiya na san cewa laifuffukan da aka fada a siyasance ne kawai kuma an yi su ne da nufin gurfanar da wanda ake ?ara da hukunta shi saboda kabilarsa, kasarsa, kuma ba a gina shi kan gaskiya ba, kuma ba a gina shi kan adalci ba.”

A bayyane, Kyari ya ce ba komai bane ke tattare da batun tuhume-tuhumensa sai dai ganin an dakushe ayyukan da yake yi na ragargazar kungiyoyin ta’addanci.

Kyari ya ce alakarsa da Hushpuppi ta fara ne a lokacin da yake tare da shi, a matsayinsa na babban jami’in ‘yan sanda, a wani samame watanni biyar kafin a kama shi Hushpuppin.

Related posts

Leave a Comment