Kano: Alkali Ya Bada Umarnin Cigaba Da Tsare AbdulJabbar

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar shekara daya kenan da fara gurfanar da Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin yin kalamai na batanci ga Manzon Allah (SAW).

Ana sane sau da dama Shehin malamin yana korar lauyoyinsa saboda sabanin da yake samu da su a yunkurin da suke yi na kare shi a wajen shari’arsa.

An ruwaito Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi kungiyar lauyoyi ta taimaka masa da wadanda za su tsaya masa a kyauta, ba tare da ya biya ko kwabo ba.

Amma a ranar Alhamis, shugaban kungiyar na reshen Kano, Barista Mukhtar Labaran Usman, ya fadawa kotu cewa ba za su iya ba malamin lauyansu ba.

Mukhtar Usman ya ce Kabara bai cancanci a taimaka masa da lauyan da zai kare shi kyauta ba domin yana karbar abin da ya zarce mafi karancin albashi a wata.

A doka, N30, 000 shi ne mafi karancin albashin da ma’aikaci zai iya karba duk wata a Najeriya. Shi dai malamin addinin ya nuna ba ya yin aikin albashin da kudi za su rika shigo masa a kai-a kai, don haka bai da tsayayyen kudin da yake shigo masa a wata.

Ganin halin da ya shiga ne sai Malamin ya bukaci a ba shi lauya da zai yi masa aiki kyauta ba tare da aljihunsa ya yi ciwo ba.

Lauyan da ya shigar da kara, Barista Yakubu Abdullahi ya roki Alkali ya ba wanda ake tuhuma aron lauya daga ofishin kwamishinan shari’a na jihar Kano. Amma malamin ya nuna bai son lauyan gwamnati, yana zargin hukuma da neman ganin bayansa, don haka ya ce ba za a kare shi da kyau a shari’ar ba.

Alkali bai yarda da lauyan gwamnati ba Shi ma Alkalin, Ibrahim Sarki Yola bai yarda a dauki lauyan gwamnati ba, ya rubutawa wani lauyan kasuwa, Dalhatu Usman takarda ya kare malamin.

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ?aga wannan shari’a, sai 9 ga watan Yuni za a sake yin zama domin cigaba da shari’ar.

Related posts

Leave a Comment