A ?alla sojoji uku ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu suka jikkata a lokacin da tawagar sojin suka taka wata nakiya da ?an Boko Haram suka birne a hanyar Maiduguri zuwa Gomboru Ngala a ranar jiya Litinin.
An ruwaito cewa tawagar bataliya ta uku ta rundunar sojin Najeriya tana yi wa matafiya rakiya ne a lokacin da ta taka nakiyar a tsakanin Gomboru Ngala da Dikwa.
A cewar wata majiya, wadda ta nemi a sakayya sunanta, “Motar sojojin ya lalace kuma mun rasa wasu dakaru sakamakon nakiya da aka birne a hanyar Dikwa/Gomboru Ngala.
“Muna addu’a Allah ya gafarta musu tare da yi wa iyalensu jaje,”.
Kazalika, wani babban jami’in tsaro ya tabbatar da “dakaru uku sun sadaukar da rayuwarsu”, ya ?ara da cewa motarsu ta lalace. “Abin ba?in ciki ne, mun rasa sojoji uku sakamakon nakiya da suka taka.
“Sun mutu a hanyarsu ta zuwa Gamboru Ngala sakamakon nakiya da Boko Haram suka birne a bangaren titin a ranar Litinin,” majiyar tsaron ya ce.
A lokacin ha?a wannan rahoton, rundunar soji ba ta fitar da sanarwa game da afkuwar lamarin ba.
