Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum ya bai wa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, lambar girmamawa ta ?asa, “de Grand Officer dans I`Ordre” sakamakon irin rawar da ya ke takawa a ya?i da matsalolin tsaro.
Shugaba Bazoum ya ce girmama Zulum ya kasance masa wajibi la’akari da namijin kokarin da Zulum ke nunawa a ya?i da Boko Haram, da damuwar da yake nunawa kan ?an gudun hijira da kokarin sake tsugunar da su a yankunansu da ya?i ya daidaita.
An gudanar da bikin karama Zulum ne a birnin Zinder, a wani ?angare na bikin ranar yanci da Nijar ke gudanawar a wannan Talatar.
Wannan shi ne karo na farko da wani shugaba a Nijar ke bai wa gwamna a Najeriya irin wannan lambar girmamawa.
Zulum ya je Nijar din ne da rakiyar Sanata kashim Shettima da ?an majalisa Mohammed Ali Ndume da kakakin majalisar jihar Borno Mohammed Tahir Monguno da wasu kwamishinoninsa.
