Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya bukaci ‘yan Najeriya su yi addu’a sannan su zabi shugabanni da suka cancanta da za su magance rashin tsaro da sauran kallubalen da kasar ke fuskanta.
An ruwaito cewa Sanusi ya yi wannan kiran ne a wurin taron kwamitin zartarwa (NEC) na Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya, Nigeria, ranar Lahadi a Abuja.
Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya, wanda kuma shine shugaban kungiyar ya bukaci yan Najeriya su hada kai don cigaban kasar ta hanyar addu’o’i.
“Abin da muke bukata shine kara hadin kan yan darika da inganta mu’amullan mu da sauran musulmi da yan Najeriya kuma mu taka muhimmin rawa don gina kasa. “Akwai bukatar mu yi addu’ar zaman lafiya a Najeriya kuma Allah ya bamu shugabanni wadanda suka cancanta kuma masu gaskiya da za su yi wa al’umma hidima, musamman yanzu da muke fuskantar zabe ga kuma rashin tsaro a kasar, ba mu da wani makami da ya fi addu’a a matsayin mu na musulmi.”
