An bayyana ?an Majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar gudummar Kawo dake yankin ?aramar Hukumar Kaduna Ta Arewa Honorable Yusuf Salihu a matsayin wanda ya zarce tsara kuma shi ne fata ga jama’ar yankin.
Al’ummar Maza?ar Kawo dake jihar Kaduna sun bayyana hakan ne a wata tattaunawa da suka yi da Wakilinmu da ziyarci yankin a makon jiya.
Sun bayyana yankin nasu a matsayin wanda ya dade cikin koma baya sakamakon rashin samun kyakkyawan wakilci, amma cikin ikon Allah samun Yusuf Salihu ya sanya sun samu karsashi da dace wanda ya yi kuma an gani domin ya kai yankin nasu ga nasara.
A zantawar da ya yi da Wakilinmu ta wayar tarho Honorabul Yusuf Salihu ya bayyana cewar damuwa da kishin jama’ar yankin gundumar Kawo shi ne a ranshi a koda yaushe, kuma hakan ne ya sanya shi sake tsayawa takara inda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP domin cigaba da ayyukan da ya fara.
