Rahotannin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce babu ?an takarar shugaban ?asa da yake mara wa baya a babban za?en dake tafe na na 2023.
Da yake magana a Minna, babban birnin Jihar Neja yayin ziyarar da ya kai wa Tsohon Shugaban ?asa Badamasi Babangida ranar Lahadi, Obasanjo ya ce Najeriya ce a gabansa ba wani ?an takara ba.
“Ba ni da ?an takara, ?asa ce a gabana,” in ji shi. “Na zo ziyarar ?an uwana da ya yi ‘yar rashin lafiya, wanda na so na yi hakan tun yana Landan amma sai ya koma gida a ranar da na isa Landan ?in.”
A makon da ya gabata, an ga Obasanjo a birnin Landan na ganawa da ?an takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da sauran ‘yan siyasa. Kafin haka, ?an takarar APC, Bola Tinubu, ya ziyarce shi a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.
